Amfani 6 da shan Bakin shayi (Coffee) ke yi a jikin Dan Adam

0

Wasu masu bincike a hukumar kula da gudanar da bincike akan cutar daji na kasa da kasa tare da babbar Kwalejin Landan(Imperial College) sun gano mahimmancin da bikin shayi ‘Coffee’ ke da shi a jikin mutum.

Masu binciken sun ce shan bakin shayi na kara taswon rayuwar mutum sannan kuma yana samar da kariya daga cututtuka kamar haka;
1. Kawar da cutar siga (diabetes).

2. Kawar da cutar koda da hanta a jikin mutum.

3. Bakin shayi na kare mutum daga samun shanyewar wani bangaren jiki (stroke).

4. Yana kawar da cutar daji a jikin mutum.

5. Bakin shayi na kare mutum daga kamuwa da cutar zuciya.

6. Kawar da cutar hakarkari.

Bayan haka wasu da suke kushe binciken sun ce yana da wuya a iya gane dangantakar da ke tsakanin samun tsawon rayuwa da shan bakin shayi domin akwai banbanci a rayuwar tsakanin mutanen dake shan bakin shayi da kuma wadanda ba sa sha.

Sun ce bakin shayi na dauke da sinadarin da ake kira Caffeine wanda kan kawo lahani a jikin mutum amma sun ce lahani da wannan sinadarin kan yi a jikin mutum ya danganta da yanayin jikin mutum ne.

Share.

game da Author