A yau Litinin ne aka bada sanarwar rasuwar Danmasanin Kano, Yusuf Maitama Sule. Ya rasu a asibitin Cairo a kasar Masar bayan ya yi da gajeruwar rashin lafiyar da likitoci a Asibitin Nassarawa, Kano, suka bayyana cewa ya na fama da ciwon kirji da kuma Nimoniya.
Ya rasu ya na da shekaru 88 a duniya. Ya yi minista sau biyu, sannan kuma ya yi takarar Shugaban Kasa a karkashin jam’iyyar NPN tare da Shehu Shagari a cikin 1979.
Bayan Shagari ya ci zabe, sai ya nada Danmasani a matsayin jakadan dindindin na Nijeriya a Majalisar Dunkin Duniya.
Kafin rasuwar sa, ya hadu da lalurar makanta tun kimanin shekaru goma da suka shude.
An haife shi a 1929, a Kano, kuma shi ne ya rike sarautar Danmasanin Kano.