Jikan marigayi Sardaunan Sokoto, Ahmadu Bello kuma Magajin Garin Sokoto Hassan Danbaba ya sauka daga sarautar Magajin Gari bayan sabani da ya samu da fadar Sarkin musulmi kan neman nada Inuwa AbdulKadir sarautar marafan Sokoto da take kokarin yi.
Hassan Danbaba ya kalubalanci cancantar Inuwa AbdulKadir kan zama marafan Sokoto, sarautar da mahaifinsa ya rike kafin marigayi Umaru Shinkafi.
Hassan Danbaba ya ce Inuwa AbdulKadir ba da bane bawa ne domin kakansa siyansa akayi.
Duk da cewa gwamnatin jihar Sokoto da Masarautar Sokoto sun karkata zuwa ga bukatar shi Inuwa AbdulKadir din Magajin Garin Sokoto Hassan Danbaba ya na nan kafe kan ra’ayinsa na rashin goyon bayan nada shi marafan Sokoto.
Bayan neman sulhu da Masarautar ta nemi yi tsananin shi Inuwa da Magajin Gari, ta nemi Hassan ya sa hannu a wata takardar da Inuwa ya rubuto don neman sulhu, Magajin gari yaki amincewa da haka inda ya ce bai gamsu da abinda wasikar ta kunsa ba.
Dalili haka Hassan ya fice da ga fadar sarki sannan ya ce a ajiye sarautar Magajin Gari da yake kai, sannan ya aiko da mota da kuma abubuwan da ke mallakin Masarautar Sokoto ne.
Daga baya Masarautar sun maida masa da su.
Kamar yadda gidan jaridar Daily Nigerian ta ruwaito wannan Labari, har yanzu Masarautar Sokoto bata fitar da wani bayani akai ba.