Dalilin da ya sa kakakin Majalisar Kano ya yi murabus kafin a tsige shi

1

Babban dalilin da ya sa tsohon kakakin majalisar dokoki na jihar Kano Kabiru RuRum ya yi murabus shine ganin cewa ‘yan majalisar sun gano wata badakalar kudi da yakai naira Miliyan 100 da ake zargin sa da karba daga hannun shahararren attajiri Aliko Dangote a matsayin toshiyar baki ga shi kansa da sauran yan majalisar domin su dakatar da ci gaba da binciken wawushe kudin masarautar Kano da ake zargin sarkin Muhammadu Sanusi II ya yi.

Duk da cewa Rurum ya karyata hakan a makon da ya gabata, da ya ga cewa ba zai sha ba da kansa yau ya sallama kujerar shugabancin majalisar.

Majisar ta nada shugaban masu rinjaye na majalisar Abdullahi Ata a matsayin sabon Kalakin Majalisar.

Share.

game da Author