YI AMFANI DA WANNAN DAMA: Rundunar Sojin Ruwa za ta fara daukar sabbin dakaru ranar 1 ga watan Yuli

0

Rundunar Sojin Ruwa na Najeriya na kira ga duk wanda yake bukatar shiga aikin sojin da ya je shafinta na yanar gizo a www.joinnigeriannavvy.com. domin cika fom din shiga.

Sharuddan da za ka cika sun hada da:

1 – Matashin da bai wuce shekara 22 ba.

2 – Wanda ya ke da shaidar kamala karatu na Diploma ko NCE kuma kada ya wuce shekara 26 wanda ya hada da ma’aikatan asibiti wato Nurses.

3 – Wanda bai da aure ne kuma dan Najeriya za nemi aikin.

4 – Kada tsawonka ya wuce mita 1.7 ga namiji, mace kuma mita 1.67

Za a bude shafin www.joinnigeriannavvy.com daga ranar 1 ga watan Yuli a rufe ranar 30 ga watan Yuli.

Karanta labarin a shafin mu na Turanci: Nigerian Navy commences 2017 recruitment

5 – Kada ka yi rijista sau biyu

6 – Ka tabbata ka yi foto kofin din shafunan da ya kunshi bada shaida na iyaye wato ( declaration and certification by parents/guardian), Shaidar karamar hukumar ka ta asali da kuma da ‘yan sanda da na wanda zai tsaya maka wato ( Local government area certificate form, Police certification form and guarantor form).

Share.

game da Author