Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Tarayya, Hon. Leo Ogor, ya bayyana cewa ba za su rika bude baki su na cece-ku-ce a majalisar tarayya ba, don kawai a ce su ‘yan adawa ne. Da ya ke tattaunawa da Premium Times, Ogor ya ce a matsayin su na bangaren adawa sun yi rawar gani a wannan shekara biyu na zangon farkon wannan mulki.
Ya ce don ka na adawa ai idan wani kudiri da aka kawo zai taimaki al’umma, bai kamata ka tashi ka kawo wa kudirin wani cikas ba. Ya ce dalili kenan za a ga cewa ‘yan adawa a majalisa sun taka muhimmiyar rawar da ya kamata a ce sun taka.
Ya ci gaba da yin nuni da cewa a daina kallon wai ba su tashi su na tayar da jijiyar-wuya a majalisa, ba haka abin ya ke ba. Ya ce su, su na magana ne kawai a kan kudirorin da shuka shafi ingata rayuwar ‘yan Najeriya, wadanda dama don haka ne aka zabe su.
Da ya juya kan mulkin Kakakin Majalisa, Ogor ya jinjina wa Hon. Yakubu Dogara wanda ya ce ya san makamar muliki da kuma iya shugabanci sosai, wanda dama haka ya kamata a ce jagora ya zama.
Dangane da batun ci gaban da suka kawo a majalisa kuwa, shugaban na marasa rinjaye ya ce ai ko yadda suka amince da wannan kasafin kudin bayan sun yi masa filla-filla ma, wani ci gaba ne. Domin a ta bakin sa, tsaikon da aka samu, matsala ce daga bangaren zartaswa, ba daga majalisa ba. Ya ce sannan ‘yan majalisa su na kokarin su wajen bin diddgin ayyukan da gwamnati ke aiwatarwa ta hanyar zagayen gani da ido kan yadda ayyukan kwangiloli ke tafiya a fadin kasar nan.
Sai dai kuma ya ragargaji masu canja sheka daga wannan jam’iyya zuwa waccan, inda ya nuna cewa ita siyasa dama ai kamar murhu ne, wasu ba su da jimirin matsawa kusa da wuta ballantana su jure kaurin hayaki har su dafa abin da za su ci ya amfane su, ya amfani jama’a. Wasu kuma komin tsananin kaurin hayaki, ba su damu ba, za su iya jurewa.