Gwamnatin tarayya ta yi gargadin bullar cutar murar tsuntsaye a Jihohi bakwai har da Abuja

0

Gwamnatin Tarayya ta bayyana bullar cutar murar tsuntsaye a jihohi bakwai har da Abuja.

Daraktan kula da cututtukan dabbobi da na kasa, da ke ma’aikatar gona ta tarayya, Gideon Mshelbwala ne ya bayyana haka a ranar Juma’a, a Abuja a lokacin da ya ke wani taro da kwamishinonin harkokin noma na jihohin kasar nan.

Jihohin da Mshelbwala ya lissafa sun hada da Bauchi, Kano, Katsina, Nasarawa, Filato. Kaduna da kuma Birnin Tarayya, Abuja. Ya ce a ranar 30 Ga Mayu din nan ne jihar Kaduna ta kawo rahoton bullar cutar a jihar.

Ya ce wannan cutar murar tsuntsaye, ta game jihohi 26 da Babban Birnin Tarayya, Abuja, ta fara bulla ne tun cikinn 2008, inda ya shafi gonakin kiwon kaji har 800 a cikin kananan hukumomi 123 a fadin kasar nan.

Ya ce har yau ba a kai ga samun wani magani na rigakafin wannan murar tsuntsaye ba. Ya da ice za a gaggauta killace wadanda ba su kamu ba, kuma ya ja kunnen cewa akwai sakacin masu kiwon kaji ta hanyar kin yin amfani da wasu dabarun kiwon kaji.

Daraktan ya ce gwamnatin tarayya ta biya kudin diyya ga wadanda kajin su su ka yi fakat har naira milyan 674 ga manomi 269 a inda annobar ta yi illa.

Share.

game da Author