Sanata Abu Ibrahim wanda mutanen mazabarsa a jihar Katsina suka yi masa ruwan duwatsu a wata ziyara da ya kai mazabar tasa ya maka wani tsohon dan majalisa Sani Liti-Yankwani a kotu akan zargin bata masa suna a idonuwar mutanen mazabarsa.
Sanata Abu Ibrahim ya zargi tsohon dan majalisar jihar da mai da shi makaryaci wanda hakan zai iya rusa masa hanyar cin abincinsa a harkokin siyasa sannan kuma hakan na iya tunzura mutanen mazabarsa su ci masa mutunci.
Ibrahim ya nuna shaidunsa da ya samo daga jaridu hudu a kotu wanda ya nuna irin maganganun da Sani Liti-Yankwani ya ke yi akan sa wanda hakan yana ci masa tuwo a kwarya.
Kotun dake sauraren karar ta daga shari’ar zuwa 3 ga watan Oktoba domin a lokacin ne lawyan da ke kare Abu Ibrahim wato Hauwa Wada za ta samarwa kotu takardun zargin da suke da shi akan Liti-Yankwani.
Bayan haka Hauwa Wada ta amince alkali Maikata Bako ya daga shari’an zuwa 3 gawatan Oktoba bayan lauyan dake kare Liti-Yankwani Alex Ajode ya roko alfarman kotun ta yi hakan shima.
Da yake tofa albarkacin bakinsa a kotun Liti-Yankwani ya ce kotun Shari’a da ke sauaraen karan da Abu Ibrahim ya shigar akansa bata dav hurumin sauraren irin wannan kara, inda yace yin haka sabawa dokar kasa ne.