Kasar Jamus ta tallafa wa Najeriya da miliyoyin kudi don kawar da cutar shan Inna

1

Najeriya da kasar Jamus sun saka hannu akan wata yarjejeniyar bada tallafin kudin ga Najeriya na euro miliyan 10 domin kawar da cutar shan inna a kasar.

Ministan al’amuran kasashen waje Geoffrey Onyeama da jakadan kasan Jamus zuwa Najeriya Bernhard Schlagheck ne suka sa hannu akan wannan takardan yarjejeniyar ranar Laraba a Abuja.

Ministan al’amuran kasashen waje Geoffrey Onyeama ya ce wannan tallafin zai taimaka wajen kawar da cutar a kasar.
Ya kuma kara da cewa har yanzu Najeriya na da sauran burbudin cutar shan inna a kasar domin aiyukkan Boko Haram a yankin arewa maso gabas.

Ya kuma mika godiyar sa ga kasar Jamus kan irin tallafi da ta ba Najeriya.

Manyan bakin da suka halarci taron sun hada da wakilan hukumar NPHCDA.

Share.

game da Author