Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya ziyarci mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo a Aso Rock.
Shugabannin biyu sun dauki tsawon awoyi biyu suna ganawa.
Bayan sun fito da ga karamin dakin taro na bangaren mataimakin shugaban kasa, Sarki Sanusi ya shaida wa manema labarai cewa ya ziyarci fadar shuagaban kasar ne domin yayi wa Osinbajo godiya a saka baki da yayi wajen dakatar da majalisar jihar Kano daga ci gaba da binciken sa da suke yi kan zargin watanda da kudaden masarautar Kano da su keyi.
Bayan haka kuma ya ce sun tattauna akan kiraye kirayen da matasan Arewa da su kayi wa ‘yan kabilar Igbo da su kwashe kayansu su koma kasar su na Biafra da suke ta likrari akai da dai sauransu.