Tsohon shugaban kwamitin kasafin Kudi na majalisar wakilai Abdulmumini Jibrin ya karyata korarsa da jam’iyyar APC na karamar hukumar Bebeji tayi yau.
Abdulmumini ya fadi haka ne a shafin sadarwarsa na Twitter da Facebook in da ya ce bashi da masaniya akan wannan Magana. Yace shima gani yayi a gidajen yada labarai.
Yace hakan shiri ne kawa domin a ci masa mutunci.
Kakakin jam’iyyar APC a jihar Kano Bashir Karaye ya ce shi bai san da wannan kora ba. A gidajen jaridu yaji hakan.
Jam’iyyar APC na karamar hukumar Bebeji, jihar Kano ta sanar da korar dan majalisa mai wakiltar Karamar hukumar a majalisar wakilai na tarayya Abdulmumini Jibrin.
Da ya ke karanta takardar korar shugaban jam’iyyar na karamar hukumar Bebeji Sani Ranka yace jam’iyyar tayi kokarin hana dan majalisar yi wa jam’iyyar zagon kasa da yake tayi amma hakan ya gagara.
Ya ce duk da cewa jam’iyyar ta kafa wata yar kwarya-kwaryar kwamiti domin a binciki wannan zargi da ake yi masa Abdulmumini ya ki halartar zaman kwamitin.
Bayan iyayen jam’iyyar sun tattauna akan abubuwan da yake yi wa jam’iyyar na zagon kasa da neman raba kan ‘ya’yan jam’iyyar ne aka yanke shawaran a yarda kwallon mangwaro ko a rabu da kuda.
Cikin abubuwan da ake zargin ya aikata sun hada da:
1 – Raba kawunan ‘ya’yan jam’iyyar
2 – Yi wa jam’iyyar zagon kasa
3 – Yin Adawa da gwamnatin Ganduje
4 – Yi wa uwar jam’iyyar na kasa rashin Kunya da shugaba Muhammadu Buhari
5 – Yi wa jam’iyyar ganin basu isa ba
Discussion about this post