Iyalan tsohon dan wasan kwaikawo Kasimu Yero sun fusata matuka kan hotunan mahaifinsu da Sanata Shehu Sani da wadansu suka saka a shafunan su na Twitter da Instagram bayan ya zitarce shi a gidansa dake Unguwar Marafa.
Iyalan Kasimu Yero sun ce abinda Sanatan ya yi bai dace ba ganin halin da mahaifinsu ya ke ciki kuma su kayi ta daukanshi hotuna a haka sannan suka saka a shafin sada zumuntarsu na yanar gizo.
Kasimu Yero da aka fi san shi a wasanni kamar ‘Cock Crow At Dawn’ da ‘Magana Jari Ce’ na fama da rashin lafiya a dan kwanakin nan.
Sanata Shehu Sani ya saka hotunan shi tare da Kasimu Yero a yanar gizo bayan ya ziyarce shi a gidansa dake Marafa Kaduna ranar Lahadi.
Sanata Shehu Sani ya ce yayi haka ne da kyakkyawar niyya amma ba wai don ya tuzarta shi ba.
Kuma ya ce sun yi hira sosai akan aiyukkansa da ya yi a aikin talabijn.
Wasu daga cikin ‘yan uwan Kasimu Yero sun yi matukar fusata ganin cewa shi kansa sanatan ya saka hotunan a shafinsa mai makon ace wai shine ma zai yi hani akan haka.
A wata takarda da wani mataimakin Sanatan ya fitar akan wadannan korafe-korafe akan abin da ya faru Suleiman Ahmed ya ce Sanata Shehu Sani ya ziyarci Kasimu Yero domin sada zumunta amma ba da wata manufa ba.
A bayanin da ya yi ya ce, “Mun ziyarci Kasimu Yero ne tare da ma’aikatan gidan jaridar Daily Trust da Rariya da kuma daya daga cikin yar sa kuma mun yi hira ne akan aiyukkan sa da ya yi na wasan kwaikwayo.
” Kasimu Yero ya nemi da Sanata Shehu Sani ya dauki nauyin sake shirya irin shirin Magana jarice domin yaran yanzu su ga yadda al’adar Hausa take tuna da. Daga nan ne sanata ya shawarci Kasimu Yero da ya rubuta bayanai akan abubuwan da ake bukata inda shi kuma zai samo wadanda zasu dauki nauyin yin hakan.
Ana shi bayanin da yayi ta da aka dauka ta naurar daukar Magana Kasimu Yero a bai san cewa wai ana daukarsa hutuna a inda yake ba. Amma ya tabbatar da ziyarar Sanata din da kuma hirar da sukayi akan sabunta shirin Magana Jari Ce.
” Bayan muntattauna da Sanata da zai tafi kuma sai ya dauko naira 100,000 ya bani sannan nayi masa godiya amma ban ce ma wani ya taimakeni da kudi ba kamar yadda ‘ya’ya na suka sanar mini cewa wai har an saka hutunana a shafaunan sadarwa a yanar gizo wai ina neman taimako.”