Hukumar kula da jin dadin Alhazai na jihar Filato ta sanar da cewa cikin maniyyata 600 da suka farayin adashen aikin haji na bana daga jihar mutane 200 ne kawai suka iya kamala biyan kudadensu zuwa yanzu.
Jami’I a hukumar Wada Haruna, ya ce har yanzu gwamnatin jihar bata tsayar da ranar da zata rufe karban kudaden maniyyan da basu karisa biya ba.
Haruna ya ce gwamnati ta ba jihar kujeru 1200 ne a hajin bana sannan Fulani makiyaya ne suka fi yawa cikin maniyyatar jihar.