Rundunar Sojin Saman Najeriya ta karyata rahoton wata gidan jarida da ta ce wai suna shirya gudanar da juyin mulki a kasa Najeriya.
Kakakin rundunar Olatokunbo Adesanya ya ce wannan magana bata da asali domin sojin saman na tare da wannan mulki na demokradiya 100 bisa 100.
‘Yan Najeriya da kasashen duniya sun gargadi sojin da kada su ce za suyi wani abinda da zai kawo cikas ga wannan mulki na demokradiyya da ake yi a kasa Najeriya.