Akalla mutane goma aka tabbatar da mutuwar su, yayin da sama da wasu arba’in suka ji raunuka lokacin da ‘yan kunar-bakin-waken Boko Haram su ka kai wasu hare-hare a kan MusulmI, lokacin da su ke gudanar da Sallar Tarawy, a ranar Laraba da dare, inda suka shigar wa garin ta kudu.
Rahoton da Premium Times ta tabbatar ya nuna cewa mafi yawan mazauna unguwar Filin Polo na Jiddari duk gudu a lokacin da aka kai hare-haren, amma daga bisani sojoji suka kai dauki, kuma suka ce kowa ya koma gidan sa.
A yayin da sojoji ke ta kokarin fatattakar mahara a unguwar Jiddari, sai wasu maharan suka samu nasarar kutsawa cikin Maiduguri ta bangaren Gamboru, ta Gabas da Maiduguri. Yayin da suka isa dauke da muggan makamai, sun kasu, inda suka rika dira masallatai daban-daban suka tayar da bam na harin kunar-Bakin-wake, ya na tashi da su da kuma wasu masallata.
Ba a dai tabbatar da yawan wadanda suka rasa rayukan su ba, sai dai kuma wasu mazauna unguwar sun tabbatar da ganin gawawwaki birjik, wadanda suka ce daga baya jami’an agajin gaggawa suka je suka kwashe su.
Wani mai gadi da ke zaman kan sa, mai suna Abba Shehu, ya ce ba ma zai iya kirga yawan wadanda suka ji ciwon da idon sa ya gane masa an kai su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri ba. A gaskiya barnar ta yi muni matuka. “Da idona na ga jama’a birjik da aka kai sun ji raunuka, yawancin su na zaune a kasa, saboda babu gadon da za a kwantar da su.
Masallacin da aka kai wa wannan hari dai ya na tsallaken hedikwatar Hukumar Raya Tabkin Chadi.
Wani da ya ga yadda abin ya faru, mai suna Alhaji Bashir, ya ce maharan su hudu ne, daya ya shiga wajen masallaci, daya ya shiga cikin Hukumar Binciken Tafkin Chadi, daya kuma cikin CBRA, daya kuma a Goni-Kachallari.
Ya ce an kai masu hare-haren ne da misalin 9 na dare, daidai lokacin da ake kammala Tarawy. Haka suka kai wadannan hare-hare a masallatan wadannan yankuna.
“Ni dai na san cewa an kwashi mutane 37 da suaka ji raunuka a yankin mu, an kais u Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri. Shida kuma a nan take suka rasu.”
Ya ce dan kunar-bakin-waken da ya kai hari a hukumar tafkin Chadi, CBDA, ya isa wajen 8:45 na dare, kuma matasan da ke gadin masu sallar sun ga lokacin da ya ke ta gudu-gudu-sauri-sauri domin ya shiga masallacin, har ma daya daga cikin matasan ya tunkare shi ya rike shi. A nan take bam ya tashi da shi da mutane uku.”
Wanda ya kai harin tsallaken ofishin Chad Basin kuwa, ya na isa wani wurin shan shayin coffee, sai ya tashi bam, ya kashe kan sa kuma ya ji wa wasu da ke masallacin kusa da shi da wasu da ke a shaguna rauni.
Harin unguwar Filin Polon Jiddari
Harin da Boko Haram suka kai ranar Laraba da dare ya hargitsa unguwar tarwe da tayar wa mazauna yankin hankali, wasu ma ba su kai ga kammala cin abinci bayan buda-baki ba, sai suka rika jin karar aman bindigogi da kuma tashin bama-bamai. Wannan ya sa kusan dukkan mazauna garin suka tsere su na shiga cikin Maiduguri.
Wani ganau mai suna Yunusa Garba, ya shaida wa Premium Times ta wayar tarho cewa, gidan sa na kusa da daidai inda aka yi artabu tsakanin sojoji da maharan Boko Haram.
“Yanzu haka da na ke magana da kai, duk gidajen makwabtan mu da ke nesa da inda aka yi harin, sun cika da wadanda suka yi gudun tsirar rai a lokacin da Boko Haram suka fara bude wuta.”
Ya ce dama kuma wasu sun sanar wa jami’an tsaro tun da rana cewa sun ga Boko Haram dauke da makamai a cikin wani kauye da ake kira Aliwadari, kusan kilomita 5 kacal kafin a shiga Maiduguri.
“An kai wa jami’an tsaro rahoton cewa an ga Boko Haram tun wajen karfe 3 na yamma, amma ba su dauki wani mataki ba.” A cewar Garba.
Tun a cikin daren da aka kai harin ne dai Gwamna Kashim Shettima ya ziyarci kauyen Alidawari.
Jamai’an tsaron da Premium Times ta tuntuba sun ce a yanzu ba za su iya tantance komai da komai ba tukunna. Haka su rundunar ‘yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin, amma ba su kara bayar da wani haske ba.