Hukumar Kiwon lafiya ta duniya WHO ta sanar da samar da wasu sabbin magunguna masu kara wa garkuwar jiki karfi ‘Antibiotics’. 30 daga ciki domin many, 25 kuma na yara ne.
Marie-Paule Kieny ma’aikaciyar kungiyar WHO ta ce hakan zai taimaka wajen bunkasa kiwon lafiyar mutane a duniya gaba daya.
Suzanne Hill shugaban sashen kula da magunguna na hukumar ta ce babbar matsalar da fannin kiwon lafiya ke fama da su yanzu shine bullowar cututtukan da basa jin magani ko da an sha.
Sabbin magungunan sun hada da:
1. Maganin cutar kanjamau wato maganin da ke hana cutar yaduwa a jikin wanda ke dauke da ita.
2. Maganin kare mutum daga kamuwa da cutar kanjamau musamman jariran dake kamuwa da cutar tun suna cikin uwayensu.
3. Maganin cutar Hepatitis C
4. Maganin cutar dajin dake kama jini wato Leukaemia da turanci.
5. Maganin cutar tarin fuka na yara da manya.
6. Maganin rage zafin ciwo ga masu dauke da cutar daji ko wace iri.