Tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida ya ce juyin mulkin da marigayi janar Sani Abacha ya yi wa Shonekan abu ne da bai ga zuwan sa ba kafin ya mika mulkin ga Shonekan.
IBB ya fadi haka ne a wata hira da ya yi da shahararriyan ‘yar jaridar nan KADARIA AHMED wanda ta yi da tsohon shugaban kasar a watan Janairun 2015.
KADARIA: Menene ya sa ka soke zaben shugaban kasa na 12 ga watan Yuli ganin cewa zabe ne wanda duk kasa suka amince da sakamakon sa?
IBB: A wannan lokacin mun sami matsalar tsaro ne a kasar sannan muna tsoron nada gwamnatin da baza ta dade ba ganin yadda ake ta cecekuce akan zaben.
KADARIA: Bayan ka nada gwamnatin rokon kwarya. Ba ka yi wa Janar Sani Abacha ritaya ba bayan sanin kwarewarsa da kayi a harkar shirya juyin mulki. Shin ko dai wata shiri ce ta boye kuka yi da ba a sani ba?
IBB: Har ga Allah ba ni da wata masaniya akan shirin Abacha a wannan lokacin. Mun bashi ne saboda a sami kwanciyar hankali sannan mutane su ga cewa Soji na tare da mulkin da aka nada.
KADARIA: Da Abacha ya yi juyin mulki ya kaji?
IBB: Na san hakan zai faru domin ‘yan siyasa suna ta yin korafi akan mulkin wanda hakan ya bashi dama ya juya gwamnatin.
Karanta labarin a shafin mu na Turanci: THROWBACK: INTERVIEW: Ex-President Ibrahim Babangida speaks on June 12 and the Abacha coup
Discussion about this post