An daina ganin gilmawar ‘yan daba a kan titinan Adamawa tun bayan wani samame da jami’an ‘yan sanda suka rika yi suna kamawa da fatattakar su a karshen watan Mayu.
A baya, ‘yan daba sun yi kaka-gida kuma sun yi zaman-dirshan a ofisoshin gwamnati da wuraren tarukan siyasa, amma a halin yanzu duk sun boye tun bayan da aka fara kama su, sanadiyya kaca-kaca da suka yi wa wasu allunan da ke dauke da hotunan gwamnan jihar, Muhammadu Bindow.
Wadannan ‘yan daba sun hasala jami’an tsaro da kuma gwamnati dangane da yadda suka kakkarya allunan masu dauke da hotuna wasu gagariman ci gaba da aka nuna Bindow ya samar a jihar a cikin shekaru biyu na mulkin sa.
Wanda hakan ne ya sa har jami’an tsaro suka kai wani samamen da suka yi nasarar cafke babban gogarman ‘yan dabar.
“Mu yanzu kawai ana bin mu ana kamawa, don haka tilas mutum ya samu wuri ya lafe, wasun mu da ba su da iyayen gida ma tuni sun bar garin.” Haka wani dan daba ya shaida wa wakilinmu., kuma ya roki ‘yan sanda su yafe musu.
Shi kuwa sakataren gudanar da shirye-shiryen jam’iyyar APC a jihar Adamawa, Ahmed Lawal, ya bayyana cewa fatattakar ‘yan dabar wani babban sauki ne suka samu a jihar musamman ga su ‘yan siyasa.
Lawal, wanda ya raba shinkafa ga wasu mata a sakatariyar jam’iyyar, ya ce da ‘yan dabar su na nan, da sun hargitsa musu wurin.
Shi ma kakakin rundunar ‘yan sandan Adamawa, Othman Abubakar, ya bayyana wa kamfanin dillacin labarai, NAN cewa tabbas sun cafke wasu ‘yan daba, wadanda ke da hannu wajen ragargaza alluran da aka karya din.
Discussion about this post