Tsohon Shugaban mai ba tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha tsaro Manjo Hamza Al-mustapha ya yi kira ga gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da ya mai da takobin ya janye sa wa da ya yi a kama shugabannin kungiyoyin Matasan Arewa da suka ba ‘yan kabilar Igbo wa’adin watanni uku su tattara inasu-inasu su koma yan kinsu.
Al-Mustapha ya fadi haka ne da ya jagoranci shugaban kungiyar MASSOB Ralph Uwazurike zuwa garin Kaduna domin neman sulhu da kungiyoyin matasan Arewan.
Al-Mustapha ya yi kira ga matasan da su dinga tauna duk abin da zasu fadi kafin su furta saboda kada ya jawo irin wannan cece kuce ko kuma ta da hankalin ‘yan Najeriya.
Ana shi jawabin shugaban kungiyar MASSOB Ralph Nwazurike ya ce kungiyarsa babu ruwa ta da Nnamdi Kanu wanda ke fafutukar kafa kasar Biafra domin shine ya kafa gidan Rediyon Biafra sannan ya ya nada shi shugabancinta amma kafin ya ankara ‘yan siyasar kabilar Igbo din su kayi kaca-kaca da manufar kafa wannan gidan Radiyo.
Ya ce ya na yi masu alkawarin cewa za su kare mutunci da lafiyar duk wani dan Arewa da ke yankin Kudu Maso Gabas din Najeriya.