Wata kungiyar mutanen jihar Akwa-Ibom ta gargadi kungiyar IPOB masu fafutikar neman kasar Biafra cewa su dai na saka jihar Akwa-Ibom a cikin taswirar kasar Biafra da suke nema.
Kungiyar ta ce babu abin da ya hada su da ‘yan kabilar Igbo.
“ Al’adar mu dabam, yarukan mu dabam, yadda muka komai na mu ba iri daya bane saboda haka suje can su ci gaba da neman kasar su ta Biafra kawai idan har ta yiwu za mu taya murna sannan muyi musu ban kwana amma ba da mu ba.”
Kungiyar ta ce ita aladunta ya yi kama ne da na mutanen yankin Kudu Maso Kudu wanda inda take Kenan yanzu amma ba ‘yan Kabilar Igbo ba.
“ Al’adun mu daya da mutanen yankinmu da ya hada da Jihohin Ribas, Cross-Ribas, Edo, Delta, da Bayelsa.”