Shugaban Muryar Najeriya (VON) Osita Ikechukwu ya sanar da cewa dole ne jam’an tsaro suyi taka tsantsan da maganar kama shugaban nin matasan Arewa da suka yi wa ‘yan kabilar Igbo da su tattara nasu- inasu su fice daga yankin.
Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai ya umarci jami’an tsaro su taso keyar shugabannin matasan tun wancan lokacin sannan ya kara nanatawa cewa komai daren dadewa sai ya tabbatar da ganin an taso keyar su.
El-Rufai ya fadi haka ne da yake karbar bakuncin shugabannin yan kabilar Igbo da suka ziyace shi a gidan gwamnati da ke Kaduna.
Osita Ikechukwu ya ce irin kuskuren da akayi Kenan lokacin da aka daure Nnamdi Kanu inda tun daga nan ne fa ya fara samun daukaka wajen ‘yan Kabilar Igbo din da yanzu ya zamo wa ‘Najeriya kaya.
Ya ce kamata yayi shugaban kabilar igbo su duba irin shelar da gwamnoni irin su El-Rufai da sarkin Katsina Maimartaba Abdulmumini Kabir da sauran gwamnonin yankin na suna tare da ‘yan kabilar Igbo din.
Ya yi kira ga shugabannin kabilar Igbo din da su yi amfani da yan uwansu da aka nada a mukaman gwamnati domin samun ci gaban yankin.