Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya ce ba zai hakura da kira da yake yi wa mutane da su canza halaiyarsu ba. Sanusi ya fadi haka ne da yake zantawa da sabon shugaban Asusun tallafawa yara na majalisar dinkin duniya UNICEF,a fadar sa dake Kano.
Sarkin yace yana da wuya mutane su yarda a wani sabon abu musamman idan sun saba da yadda suke a ko ina ne a fadin duniya.
“ Amman a sani cewa akwai mutane da yawa da suka fahimci inda na dosa kuma suna tare da ni. Saboda haka ina kira ga kungiyoyi, Dalibai, ma’aikatu da malaman addini da su mara mini baya akan irin canji da nake so in kawo wa Al’umma.
Kuma na san zan samu nasara akan haka domin abune mai kyau nake yi wa al’ummar.
Bayan haka kuma Sarkin ya kalubalanci iyaye da su mai da hankali wajen ba wa ‘ya’yansu tarbiyya nigari domin rashin haka ne yakan kawo matsalolin fyade da akeyi wa yara kanana da dai sauransu.
Shugaban ‘UNICEF’ na kasa Najeriya Mohammed Fall ya godewa wa sarkin da irin karramawar da yayi musu kuma ya ce UNICEF za ta ba Sarki duk irin gudumnawar da yake bukata domin samun nasara akan aikin da ya sa a gaba.