Jami’an tsaro na SSS sun cafke ‘Yar wasar Kannywood shekara 6 bayan ta gudu daga gidan Yari

0

Jami’an tsaro na Sirri da na gidajen Yarin Najeriya sun kama ‘yar wasan Hausa Rabi Ismail shekaru shida bayan ta gudu daga kurkukun Hadejia dake Jihar Jigawa.

Ita dai Rabi da aka fi sani da Rabi Cecelia an yanke mata hukuncin kisa ne ta hanyar rataya a shekarar 2011.

Kotu ta yanke wannan hukunci ne bayan kamata da laifin kisa da tayi wa wani tsohon saurayinta mai suna Auwal Ibrahim a Kano.

Ana zargin Rabi da saka wani guba a cikin alawa da ta ba saurayin nata inda daga bisani kuma ta tunkuda shi cikin kogin Tiga.

Hakan ya faru ne a 2002.

Bayan an gurfanar da Rabi a Babbar kotu da ke Kano, kotu ta tabbatar da laifinta sannan ta yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya.

An yi ta daukaka karar domin ganin hakan bai tabbata akanta ba amma ba ta sami nasara ba.

Bayan an daure ta ne a kurkukun Hadejia sai ta ko gudu a shekarar 2011 wanda sai yanzu aka sake kama ta.
Yanzu dai tana tsare a hannun jami’an tsaron.

Share.

game da Author