TAMBAYA: Menene asali da faidar wannan Aya “INNA KAFFAINA KAL MUSTAH ZI’IN” Tare da Imam M Bello Mai-Iyali

0

TAMBAYA: Mallam ina son kayi mun bayani akan asali da kuma faidar wannan addu’ar “INNA KAFFAINA KAL MUSTAH ZI’IN”? Allah ya karawa malam lafiya da nisan kwana

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi
Muhammad SAW.

Ina fatan dan uwa ka na biye damu a cikin wannan shafi mai Albaka, “INNA KAFFAINA KAL MUSTAH ZI’IN” wannan fadin Allah ne a cikin Alkur’ani Mai Girma Suratul Hijr, sura ta goma sha biyar (15), Aya ta 95. In da Allah ya ke rarrashin Annabin sa Muhammad (SAW) ya ke cewa: “إِنَّا كَفَيْنَاكَ الْمُسْتَهْزِئِين” ma’anarta she ne “ Lallai za mu kareka ga masu izgilanci”.

Wannan aya tana cikin ayoyi guda biyar na karshen wannan sura, kuma asalin su she ne, Allah ya umurci Annabin sa (SAW) da bayyana kira zuwa ga addinin musulunci ga kowa kuma abayyane, dukk da cewa ana tsangwamar sa kuma ana cutatar da shi sabo da addinin. Sai Allah ya umurcesa da bayyanar da addinin kuma ya yi masa alkawarin kareshi daga
dukk wani azzalumi. Wannan she ne dalilin fadin Allah “Inna Kaffaina Kal Mustah Zi’in” “ Lallai za mu kareka ga masu izgilanci”.

Hakika Allah ya kare manzonsa daga dukkanin sharrin masu cutarwa kuma ya kunyatar da su, ya kaskantar da su, sun mutu a wulakance . ImamulTabari ya ruwaito gada Ibn Abbas cewa masu izgilanci ga manzo (SAW) su takwas ne daga cikin manyan masu iko a cikin kuraishawa, kuma dukk Allah ya halaka su kafin yakin badar.

FA’IDA

Al-kur’ani waraka ne ga zuciya da ganganjiki. Ya hallata a yi tawassuli/tabarruki da karatun Alkur’ani, ko wani bangare daga cikin sa, ko sura daga cikin sa, ko aya don samun waraka ko kariya ko tsari. Kamar yadda ya tabbata a sunnan Annabi (SAW) ana karanta fatiha, ko falaki da nasi, don neman tsari, ko kariya ko waraka daga cuta.

“Inna kaffaina kal mustah zi’in” “إِنَّا كَفَيْنَاكَ الْمُسْتَهْزِئِين” Masana sirrin Alkur’ani sun ce anna tabarruki da wannan Aya, domin
kariya daga makiyi ko abokin gaba. Duk bawan da yake son Allah ya kareshi daga sharrin makiyi ko abokin gaba, to, yalazimci karanta wannan aya.

Allah zai bada kariya idan an karanta wannan aya kafa 1,000 ko 1,200 a wani kaulin. Sai dai manyan malamai suna kyamar baba yawan adadi ga wani zikiri ko addu’a, matukar dai hakan ba daga nassi ba ne.

Ana bukatar bawa ya yi zikirinsa ko addu’ar sa da yawa gwar-gwadon iko, kuma ya dage sannan ya dogara ga Allah. To, Allah ya na kusa kuma ya na jin bukatun bayinsa, zai biya bukatun sa. Amma sanya wani adadi na musamman ga zikiri ko addu’a ba tare da nassi ba, to kuskure ne a wajen wasu malamai.

Ya Allah! Ka karemu daga cutarwan makiya. Amin.

TAMBAYA: Menene matsayin wanda ake binshi/ta azumi bara kuma har na bana ya zo bai rama ba. Shin Zai iya ciyarwa ko kuma dole sai ya rama. Haka macen da take shayarwa , zata iya ciyarwa ko kuma dole sai dai ta rama azumin.

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Mutumin da ake binshi azumin bara, kuam bai rama ba har na bana yazo, ya nada hukunci kamar haka:

1) Mustahabbi ne gaggauta ramakon azumi ga dukk wanda ya sha azumi.

2) Wajibi ne ramakon azumi ga dukk wanda ya sha azumi, idan kwanakin Ramadana mai zuwa su ka rage dai-dai adadin kwanakin da sha. Misali: wanda ya sha azumin kwana uku, bai rama ba, har Sha’aban din bana ya rage saura kwana uku kacal ya kare. To, wajibin sa ne ya rama su cikin waddannan kwanaki uku.

3) Dukk wanda ya yi jinkirin ramakon azumi har wani Ramadana ya zagayo, ba tare da wani karbabben uzuri ba, kamar rashin lafiya, to, ya yi mummunan aiki, kuma ya saba umurnin Allah.

4) Zai rama adadin kwanakin da ya sha, kuma zai ciyar da miskini a adadin wannan kwanakin.

Wanda ya yi sakaci, har ramadanan bana ya zo, bai rama ba, bai rama na bara ba, Dole ya rama azumin kuma dole ya ciyar da miskini.

Imam Malik, Imam Shafi da Imam Ahmad, da sauran mayan malaman doniya sun bada wannan fatawan riko da Hadisin Ibn Abbas wanda Darul Kudiniyyu ya ruwaito: “Wanda ya yi sakacin ramakon azumin Ramadana, har wani Ramadana ya za gayo bai rama abinda ya sha ba, to, ya rama kwanakin da ya sha kuma ya ciyar da miskini a ko wane yini”.

Hakika macen da take shayarwa, zata sha azumi idan tana jin tsoron zata tagayyara ko kuma dan da ta ke shayarwa zai tagayyara.

Mai shayarwan da ta sha azumi don tsoron tagayyar ta ko na danta. Dole ne ta rama azumin kuma dole ta ciyar da miskini, bisa fatawar manyan malamai.

Lallai Allah SWT ya fada a cikin Al-kur’ani cewa: Lallai yin azumi shi ne mafi alkhairi ga duk masu ikon yin azumin.

Allah shi ne mafi sani.

Share.

game da Author