Minister Harkokin Kudi, Kemi Adeosun ta bayyana cewa Nijeriya ta kama hanyar fita daga halin matsin tattalin arziki da halin kaka-ni-ka-yi da ake ciki.
Kemi ta yi wannan jawabi ne a wurin wani gagarimin taron jin ra’ayoyi da amsa tambayoyin jama’a, wanda wasu ministoci suka shir ya, da yanzu haka ake cikin gudanarwa a Abuja.
Sauran Ministocin da ke wurin sun a amsa tambayoyin jama’a, sun hada da: Ministan Makamashi, Ayyuka da Gidaje, Fashola, Audu Ogbe Ministan Harkokin Noma, Lai Mohammed Ministan Yada Labarai, Udoma Udoma Ministan Kasafin Kudi da kuma Janar Dambazzau, Ministan Harkokin Cikin Gida.