Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutane takwas a jihar sanadiyyar kamuwa da cutar sankarau.
Kwamishinan kiwon lafiyar jihar Paul Dogo ya tabbatar da haka da yake zantawa da manema labarai ranar Litini a Kaduna.
Paul Dogo ya ce tun bullowar cutar a watan Janairu zuwa yanzu jihar ta sami rahotan bullowar cuta mai kama da haka akan mutane 68 in da aka tabbatar da mutane 11 sun kamu kuma 8 daga ciki sun rigamu gidan gaskiya.
Mutane takwas din da suka rasu kuwa ‘yan asalin kananan hukumomin Kaduna ta kudu, Kaduna ta Arewa, Igabi da karamar hukumar Giwa.
Paul Dogo ya ce gwamnatin jihar Kaduna na iya kokarinta domin ganin cutar bata yadu ba asauran sassan jihar ta hanyar horas da ma’aikatan kiwon lafiya da bada da kula ta musamman ga mutanen jihar.