RAHOTO NA MUSAMMAN: Tsadar shinkafa: Ko dai laifin ‘yan kasuwa ne?

0

Ministan Harkokin Noma Audu Ogbe, ya bayyana dalilin da ya sa shinkafar da ake nomawa a Nijeriya ta fi wacce ake shigowa da ita tsada. Ministan ya yi bayanin ne a ranar Talata, a wurin wani gagarimin taron da ministoci suka hada domin sauraren koke-koke, shawarwari da kuma amsa tambayoyin jama’a, da a Turance a ke kira townhall meeting.

A lokacin da yake amsa wata tambaya, Ogbe ya ce babban dalilin da ya sa shinkafar gida ta fi ta waje tsada shi ne kasashen da ake shigo da shinkafa su na yin rangwamen tallafi ga shinkafar da su ke saIda wa kasashen waje, subsidy a Turance.

Ya ce yawancin shinkafar nan ana shigo da ita ne daga kasashen Vietnam, India da Thailad. Ya ce kasar Thailand ta na yin rangwamen haraji sosai a kan shinkafar da su ke sayarwa ga kasashen waje irin Nijeriya.

Ya kuma bayyana cewa shinkafar da ‘yan kasuwa ke shigo da ita a Nijeriya, ta na isowa har cikin kasar nan kan naira dubu 9 a kowane buhu daya, su kuma su saida naira dubu 13 a kan kowane buhu daya, sabanin yadda ake saida buhun shinkafar gida a kan naira 16.

Wani dalilin kuma da ministan ya bayar, shi ne tsadar kudin ruwa da bankuna ke dora wa masu karbar lamunin kudi a banki domin su yi noma.

“Kudin ruwa da bankunan mu ke dorawa ya fi na sauran yawancin kasashen duniya yawa kwarai da gaske.” Cewar Audu Ogbe.

Tsadar shinkafa: Ko dai laifin ‘yan kasuwa ne?

Yayin da ministan harkokin noma Audu Ogbe ya bayyana cewa naira 13 ‘yan kasuwa ke saida buhun shinkafa, wani binciken kai-tsaye da PREMIUM TIMES HAUSA ta gudanar a yau ya bayyana irin yadda ministan ko dai bai san takamaimen farashin shinkafa a kasuwa ba, ko kuma yadda ya bayyana din ke gaskiya, amma su kuma ‘yan kasuwa su na tsawwala wa jama’a dan karen tsada.

PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa a Kano kananan kantuna na cikin unguwanni da lunguna su na saida buhun shinkafa ‘yar Thailand naira dubu 16,500 zuwa naira dubu 17,000. A kan samu inda ma ake sayarwa a kan naira dubu 16,000.00.

Sai dai abin mamaki, a cikin manyan kantunan alfarma, wato super markets da ke Abuja, ana sayar da buhun shinkafa har naira dubu 21,500.00, yayin da a kasuwa da kuma wasu kantuna kamar Sahad Stores, ana sayar da buhu daya a kan naira dubu 18,500.00.

Haka kuma binkiken PREMIUM TIMES HAUSA ya tabbatar da cewa a Kano ana sayar da karamin buhun shinkafa naira dubu 8,500, yayin da ake saida shinkafa ‘yar Hausa a kan naira dari 850 kowace tiya, wato mudu biyu kenan. Buhun ta kuma ana sayar da shi naira dubu 35,000.00 zuwa dubu 36,000.00, tunda mudu 80 ne, sabanin ‘yar Thailand mai yin mudu 36 (mudu biyu ne kwano/tiya daya).

Rice b

Matsalar tsadar kayan masarufi dai ta zama ruwan dare a Nijeriya, musamman a cikin birane, inda yawanci ake dora laifin abin akan gwamnati, wasu kuma a kan hauhawar farashin Dalar Amurka, wacce da ita ake sayo kayan masarufin a kasashen waje.

Dimbin jama’a kuma na dora laifin tsadar kayan masarufi a kan ‘yan kasuwa masu son yin kudi a dare daya, ta hanyar dora riba mai tarin yawa a kan dukkan kayan da talakawa ke bukata na gudanar da rayuwar yau da kullum.

A gefe daya kuma akwai masu dora laifin a matsayin ragwancin ‘yan Nijeriya da su dai sun fi son abin da aka shigo da komai daga waje, maimakon su farka daga barci su rika nomawa ko sarrafawa a kasar nan. Binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar a yau Talata, ya tabbatar da cewa a yau hatta tsinken sakace da tsinken tsire duk ana shigo da su daga China.

Baya ga wadannan, wani binciken kuma ya tabbatar da yadda ake samun bambancin farashin kayan masarufi a tsakanin ‘yan kasuwa su ya su. Misali, wani sabulun gyatuma-radau ko maida-tsohuwa-yarinya da mata ke wanka da shi domin fatar su ta yi fes, wato Crusader, kafin tsadar kayan masarufi ana sayar da shi naira 300 kacal.

Sai dai kuma wani binciken gaggawa da PREMIUM TIMES HAUSA ta gudanar, ta tabbatar da cewa manyan kantunan alfarma da ke Abuja irin su H. Medix, Spa, Shoprite da sauran irin su birjik, duk su na saida wannan sabulu kwaya daya naira dari 750 a yanzu.

Abin mamaki, idan mutum ya shiga kasuwanni irin su Wuse Market, Garki Market da sauran su, zai samu wannan sabulun naira 500, wani wuri ma har naira 450.

Yayin da PREMIUM TIMES ta gano cewa wasu manyan kantunan a cikin kasuwa su ke sayo kaya a hannun manyan diloli, wani binciken kuma ya nuna cewa yawancin wadannan manyan kantuna duk holoko ne, ba jari gare su ba, sai dai su kama haya, manyan diloli su rika damfara musu kaya, idan sun sayar su rika biyan balas.

Ba mamaki saboda su na biyan haya da dan karen tsada ne ya sa su ke tsawwala wa kayan da ake shigo da su farashi mai zafin gaske. Baya ga tsada kuma ga kudin lantarki, albashin ma’aikata da masu karbar kudi, masu kula da kaya, masu gadi da sauran su. Shin ko duk a jikin talaka ko kwastomomi wadannan manyan kantuna ke fitar da albashin wadannan ma’aikata da kudin haya har su dora riba?

Za a yi mamakin yadda kayan masarufi na gida Nijeriya ke da arha tibis a cikin wadannan kantama-kantaman kantinan kayan masarufi. PREMIUM TIMES HAUSA ta gano cewa a cikin Spa, Shoprita da wasu kantinan, farashin lemon kwalba bai kai naira 100 daya ba, alhali kuma a waje hatta kananan kantina naira 150 su ke sayar da shi.

Ba lemun kwalba ba, hatta ruwan sha na cikin kwalaben roba da ake sarrafawa a nan Nijeriya sun fi arha a cikin wadannan manyan kantina. Tambaya a nan ita ce, shin dole sai an yi amfani da kayan masarufin kasashen waje?

Akwai amsa ko mu shekara tambayar juna?

A wani jirwaye mai kama da wanka kuma, ministan harkokin noman har ila yau dai ya ce, gudun noma ke ke sa ‘yan Nijeriya shigo da abin da mu ke iya nomawa.

Ministan Harkokin Noma Audu Ogbe, ya bayyana cewa ragwanci da rashin kishin wasu manyan mu da ba su son zuba jari a harkokin noma ya sa mu ka wayi gari mu ke dogaro da shigo da kayan abinci daga kasashen waje.

Audu Ogbe ya yi wannan jawabin ne yanzu haka a wani taro na kai-tsaye da ministoci suka shirya domin jin ra’ayoyin jama’a tare da amsa tambayoyin su, da ake gudanarwa yanzu haka a Abuja.

Audu Ogbe ya buga misali da abin da ya kira abin takaici da Nijeriya ke kashe sama da Dalar Amurka milyan 100 a duk shekara, wajen shigo da tumaturin gwamngwani, wanda ya ce wani sinadarin tumatur din ma cutarwa ya ke yi maimakon amfana wa jama’a.

Share.

game da Author