Ma’aikatar kiwon lafiya ta yi gargadi kan illolin da ke tattare da matsanancin yunwa da ake fama dashi a wasu sassan kasa Najeriya.
Jami’in ma’aikatar Chris Isokpunwu ya fadi hakanne a wata taron wayar da kai da akayi domin samarda hanyoyin da za’a iya bi domin kawar da wannan matsala ta yunwa musamman ga yara kanana wanda su ne yafi addaba.
Anyi wannan taro ne a jihar Enugu dake kudancin Najeriya.
Chris Isokpunwu ya ce Najeriya na bukatan kudaden da ya kai Naira biliyan 279.54 domin samar da wadataccen abinci ga yankunan dake fama da yunwa a kasar.
Yayi kira ga gwamnatin tarayya da wadansu kungiyoyi masu zaman kansu da su hada kai domin samar da wadannan kudade da za’ayi aiki dasu har na tsawon shekaru biyar masu zuwa.
Chris ya ce a lissafinsu wadannan kudade idan har aka samar dasu zai taimaka wajen kawo karshen wannan matsala da samar da abinci ga yara kanana da suka kai 123,000 sannan wasu 890,000 zasu sami abincin da zai taimaka musu wajen gina jiki da inganta girmansu kamar yadda ya kamata.
A wata Bincike da aka gudanar ya nuna cewa kasar India ce tafi kowace kasa a duniya yawan yaran da suke bukatar kula ta musamman da ya shafi ciyar da su abinci domin kawar da matsanancin yunwa a kasar.
Bayan haka kuma bayanan ya nuna cewa Kasa Najeriya ce ta ke sahun na biyu a jerin kasashen da yara musamman ‘yan kasa da shekara biyar dake fama da matsanancin Yunwa a duniya.
Majalisar dinkin duniya ta ce matsanancin yunwa fitina ne da ke daukar rayukan mutane a hankali.
Ta yi ikirarin cewa yankin arewa maso gabas din Najeriya na da akalla yara miliyan 2.4 da ke fama da matsanancin yunwa.
Majalisar ta ce a yanzu haka Asusun kula da bada tallafi ga kananan yara UNICEF tare da wasu kungiyoyi masu zaman kansu na kula da 600,000 zuwa 800,000 na yaran da ke fama da yunwa sannan kuma gwamnatin Najeriya za ta biya Naira biliyan 95 a shekaran 2017 domin kula da yaran.