Kungiyoyin sa-kai sun nemi a yi binciken harkallar daukar jami’an SSS

0

Kungiyoyin sa-kai sun yi kira da a gaggauta yin binciken yadda aka yi harkallar daukar jami’an SSS, inda suka bayyana tsarin da aka bi a matsayin haramtaccen tsari kuma gwamnatin tarayya ta karya sharuddan daukar ma’aikata.

Manajan kungiyar Resource Centre for Human Right, Armsfree Ajanaku, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta sake duba wannan lamari har ma da sauran wasu shirin daukar ma’aikatan da aka gudanar a baya-bayan nan domin a tabbatar da cewa an yi wa kowane yanki adalci.

Ajanaku ya kara da cewa wannan harkalla ta daukar ma’aikata ta nuna a fili cewa har yanzu dai ba a rabu da Bukar ba, a irin murda-murdar da aka rika yi a gwamnatocin baya, duk kuwa da cewa ana maganar gwamnatin canji a yanzu.

“Irin wannan harkalla ba wani abu ta ke kara rurawa ba, sai wutar kabilanci da bangaranci wanda ka iya zama barazana ga zaman taren wannan kasa tsakanin kabilu da jihohi daban-daban.

Shi kuma Lanre Suraj na CSNAC, ya ce za su tunkari hukumar daukar ma’aikata ta kasa, domin a bisa dukkan alamu har yau abin dai bai canja zani ba.

Idan ba a manta ba, Premium Times Hausa ta kawo rahoton zargin aringizon da aka yi wa wasu jihohi kamar Katsina, da wasu jihohin, yayin da aka yi wa wasu kwange a fannin daukar jami’an tsaro na SSS watannin baya.

Share.

game da Author