Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta ce ba kamar yadda ake ta yayadawa ba cewa wai shugaban Kasa Muhammadu Buhari na nan kwance ko abinci baya iyayi ci, Ta ce yana nan da kuzarinsa domin a yau ma ya gana da wadansu jami’an gwamnati.
Aisha ta sanar da hakanne a shafinta na twitter in da ta kara da cewa shugaban kasan yana samun lafiya akullun wayewar gari.
“ In godiya ga ‘Yan Najeriya kan nuna damuwarsu da suke yi game da rashin lafiyar mijina. Kuma ina so in sanar da kowa cewa ba kamar yadda ake ta yayadawa ba, Buhari na nan da kuzarinsa.