Majalisar Kano ta dakatar da ci gaba da binciken Sarkin Kano Sanusi

0

Majalisar dokokin jihar Kano ta sanar da dakatar da ci gaba da binciken da takeyi wa masarautar Kano.

majalisar na bincike Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II kan zargin kashe kudaden masarautar ba a ka’ida ba.

A wata wasika ta musamman da gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya aika majalisar ya ce wasu manyan kasar nan ne suke rokeshi da ya sa baki a kan binciken da akeyi wa sarkin.

Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, tsohon shugaban Kasa Ibrahim Babangida, Amince Dantata, Aliko Dangote, Sarkin Musulmi Abubakar Sa’ad na daga cikin wadanda suka roki majalisar da ta dakatar ta binciken a kan sarkin.

” Sarkin Kano Sanusi ya amince da duka kurakuransa kuma ya roki gafara sannan ya ce zai gyara. Saboda haka naga lallai ya kamata a hakura domin a sami zaman lafiya a masarautar da jihar baki daya.

Ganduje yace duk da cewa bai so ya sa ka baki a maganar binciken ba ya zama dole yanzu ganin yadda manyan kasa suka nemi yayi hakan.

Share.

game da Author