Mu mai da hankali wajen bunkasa fannin ilimi a kasar nan – Inji Sarki Sanusi

0

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga gwamnatin tarayya da na jihohi da su hada kai da ‘yan kasuwa masu zaman kansu domin su zuba jari a kasa Najeriya don bunkasa musamman fannin wutan lantarkin kasa.

Ya fadi haka ne a taron bikin cika shekaru 50 da kirkiro jihar Kano a garin Kano.

Sarkin ya ce karancin wutan lantarkin da kasa ke fama da shi ne ya hana mafi yawa-yawan masana’antun kasarnan aiki.

Ya ce gyara fannin wutan lantarkin kasa  zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da kuma ci gaban jihar Kano da kasar baki daya.

Bayan haka Sarkin Kano ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta ci gaba da wadata fannin ilimi da tallafin da take bukata musamman wanda ya shafi yara kanana da mata.

 ‘’Ilimi itace mabudin ci gaban. Ya kamata mu mai da hankali sosai wajen ba wannan fannin tallafin da yake bukata domin ci gaban al’ummarmu.”

Bayan haka kuma ya roki gwamnati da ta mai da hankali wajen bunkasa ayyukan gona da sauran su.

Share.

game da Author