Kotun Koli ta yi watsi da rokon PDP bangaren Sheriff

0

Kotun Koli ta Nijeriya ta yi watsi da hanzarin da shugaban bangare daya na jam’iyyar PDP, Sanata Ali-Modu Sheriff ya yi cewa kada kotun ta saurari karar da bangaren Sanata Ahmed Makarfi ya kai a gaban ta.

Shi dai Sanata Sheriff, ya kai karar ne, inda ya roki kotun kada ta saurari karar da Ahmed Makarfi ya kai a gaban ta, inda ya shigar da karar da ya daukaka sakamakon hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta Fatakwal ta yanke a ranar 17 Ga Fabrairu, cewa Sheriff shi ne halastaccen shugaban jam’iyyar PDP.

A sauraren karar da aka fara yau a Abuja, lauyan Sheriff, Akin Olujjimi, ya ce wa kotun, karar da Makarfi ya shigar ta karya ka’idar shari’a, domin bai nemi kotun daukaka kara ya shaida mata cewa zai garzaya kotun koli ba, sai ya tafi kai-tsaye. Don haka sai ya roki kotu da ta yi watsi da karar da Makarfi ya kai.
Da ya ke maida martani, lauyan Makarfi, mashahurin lauya Wale Olanipekun, ya roki kotu ta tsaya ta saurari karar da Makarfi ya kai, inda ya ce maganar lauyan Sheriff ba ta ma da wani tushe balle dalili.

A dan kwarya-kwaryan hukuncin da alkalan kotun kolin su ka yanke, sun ce karar da Makarfi ya shigar ta na bisa ka’ida, domin lauyoyin sa sun shigar da karar ne kafin wa’adin watanni uku da alkalin kotun daukaka kara na Fatakwal ya yanke cewa zai iya daukaka kara a cikin watanni uku.

Babban Cif Joji na Tarayya, Walter Onnoghen shi ne ya jagoranci sauran alkalan da ke zaman gudanar da wannan shari’ar wadda aka fara saurare a yau Litinin a Abuja.

Onnoghen ya ce, Kotun Koli ta Tarayya ta zartar da hukunci cewa duk karar da za a daukaka, to a tabbatar an daukaka karar kafin watanni uku su cika bayan yanke hukuncin shari’ar da za a daukaka.

Ya kara da cewa su kuma a Kotun Koli, su na la’akari ne da cewa kotun daukaka kara ta yanke hukuncin ne tun a cikin watan Fabrairu, yayin da Makarfi kuma ya shigar da kara ne tun kafin wattanni uku na wa’adin ya cika.

Da ya ke ba a kai ga tashi kotun ba a lokacin da PREMIUM TIMES HAUSA ke rubuta wannan labari, za mu ji ranar da za a ci gaba da zaman shari’ar,

Share.

game da Author