A rahoton da cibiyar ‘Center for Democracy and Development’ ta fitar da safiyar litinin din yau ya nuna yankin Arewa maso Yamma ne suka fi yawan mutanen da suka nuna amincewarsu da ayyukan wannan gwamnati shekara biyu bayan rantsar da ita.
Rahoton ya nuna cewa kashi 85 bisa 100 na mutanen da ke yankin Arewa Maso Yamma da kuma kashi 66 bisa 100 na mutanen da ke Arewa Maso Gabas ne suka yaba wa ayyukan da wannan gwamnati tayi zuwa yanzu wanda a iya yawan mutanen da suka fadi ra’ayinsu akan hakane ya bada kashi 5 bisa dari na lissafin da cibiyar ta yi.
Sama da kashi 75 na mutanen yankin Kudu sun zabi akasin haka ne.
Sun ce basu yarda an sami wani ci gaba da har wannan gwamnati zata yi bugun kirji akai ba.