Jiragen saman Kenya basu kyauta ba dawowa da gawar wani dan Najeriya da su kayi – Ministan Kiwon Lafiya

0

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya nuna rashin Jin dadin sa yadda kamfanin jiragen sama na Kenya Airline’ suka shigo da gawan wani dan Najeriya daga kasar Kongo da tayi ba tare da samun cikakken izinin yin haka ba.

Ministan ya ce abinda suka yi bai dace ba ganin cewa kwanannan ne ake ta kokarin samar da rigakafin cutar Ebola a kasar saboda barkewar cutar.

Ita dai jirgin saman ta sauka ne a filin sama na Murtala Muhammed dake Legas dauke da gawar wani mutum sannan ta ajiye shi. Ko da yake bayanai ya nuna cewa an gwada gawan kuma bata dauke da cutar Ebola wanda hakan ne ya sa aka shigo da shi kasar.

Bayan haka hukumar kula da cututtuka na kasa NCDC tare da babbar asibitin koyarwa na jihar Legas sun tabbatar da cewa babu cutar Ebola a jikin gawan.

Daga karshe ministan kiwon lafiya ya bada umurnin amfanin da na’urori domin binciken matafiyan da suke shigowa kasa Najeriya.

Share.

game da Author