A yau Talata ne wani dan kunar bakin wake ya ta da bam gidan rawa ta Manchester dake kasar Britaniya inda akalla mutane 19 suka rasa rayukansu sannan mutane 50 suka jikkita.
A wata bidiyon da wani ya dauka an ga cewa bam din ya tashi ne yayin da ake shirin kammala holewar da mawaka sukeyi wanda hakan ya jefa mutane musamman yaran da basa tare da iyensu a lokacin da bam din ya tashi cikin wani halin rudani.
‘Yan sandan sun ce wani dan kunar bakin wake ne ya dasa bam bam a filin kuma shi ma ya mutu a sanadiyyar tashin ta.
Bam din ya tashi ne bayan mawakiya Ariana Grande, ta gama nata rawar.
Shugaban gwamnatin kasar Britaniya Theresa May ta nuna matukar rashin jin dadinta akn abin da ya faru sannan ta ce karsar Britaniya baza tayi kasakasa ba wajen ganin hakan bai sake faruwa ba a kasar.
Gwamnatocin kasashen duniya sun nuna fushinsu da yin juyayi akan wannan hari da aka kai garin Manchester.
Bayan haka gwamnatin kasar Britaniya ta sanar da rufe tashar jirgin kasa dake garin na Manchester Victoria kuma Theresa May ta kira taron gaggawa na jami’an gwamnati sannan ana sa ran zata ziyarci garin na Manchester yau.