Nuna halin ko in kula da akayi ne ya sa cutar Ebola ta ke neman ta sake yaduwa – WHO

0

Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta koka da nuna halin ko in kula da akayi wajen shawo kan cutar Ebola da ta bullo tun a shekarar 2014 a yammacin Afrika.

Shugaban hukumar WHO Margaret Chan ta nuna rashin jin dadinta da yadda cutar ta sake bullowa a kusa da iyakar kasan dake jamhuriyan Kongo da kuma tsakiyar jamhuriyan Afrika.

Ta fadi hakan ne a taron wayar da kai akan kiwon lafiya ta duniya na karo 70 da aka yi a Geneva.

Margret Chan ta ce kasashen duniya 194 da suka halarci taron za su tattauna akan matsalolin da ya shafi kiwon lafiya da darussan da aka koya.

Ta kuma ce wasu kwararru za su kawo bayanai akan yadda kasar Angola ta shawo kan cutar zazzabi shawara wanda ake kira ‘Yellow Fever’ da ta bullo a kasar a shekarar bara da yadda za a shawo kan cutar amai da gudawa da ta bullo a cikin kwanaki biyu da suka wuce a kasar Yeman da kuma yadda za a tura ma’aikata domin kawar da cutar shan inna a kasashe uku wanda suka fi fama da cutar da ya hada da Najeriya,Afghanistan da Fakistan.

Daga karshe kasashen duniyan da suka halarci wannan taron za su zabi sabon shugaban hukumar a ranar Talata daga cikin ‘yan takaran da ya hada da Tedros Ghebreyesus daga kasar Ethiopia, David Nabarro daga kasar Turai da Sania Nishtar daga kasar Fakistan.

Share.

game da Author