kakakin shugaban kasa Mal. Garba Shehu ya ce gwamnatin Najeriya ta na ci gaba da tsare shugaban kungiyar Shi’a Ibrahim El-Zakzaky ba don komai ba sai don ta samar masa da tsaron da yake bukata.
Garba shehu ya ce sakin El-Zakzaky zai iya zama hadari ga lafiyarsa da rayuwarsa har da na iyalansa.
Ya ce sakin Ibrahim El-Zakzaky zai iya tada zaune tsaye sannan kuma ya sanya rayuwarsa da lafiyarsa cikin mummunar hadari.
“Hakin gwamnti ne ta tabbatar ta bashi duk irin kariyar da yake bukata hakan ne yasa muka ga yafi a barshi a inda zai zamu natsuwa da kariya.”
“Daurin da aka yi masa ba irin wanda ake zato bane kamar daurin kurkuku, gwamnati ta ajiyeshi kariya ga rayuwarsa da lafiyarsa. Kuma ya na ganawa da iyalansa duk yadda yake so.”
Discussion about this post