Duk wanda kaga ya gagara wuri ya Samu.
Da Dan Kuka ya tono tsuliyar dodo garin magarya ta gagareshi Zama.
A sanadiyyar rashin jinsa ankusa a kara yi wa ubansa kaciya duk da ya sha da kyar amma da balli-balli.
Daga karshe dai Dan kuka gudu ya daga garin magarya inda ya fantsama birni.
To fa, ko yaya za ta kaya da Dan kuka a birni? Gashi kuma tawagan barada sun shigo birni nemansa.
A sababbin hotunan da Muka Samu ta shafin Jarumi Zaharaddeen Sani ya nuna cewa yanzu ne ma aka bude sabuwar faifai a wannan shiri.
Jarumai a sabon shiri: Falalu Dorayi, Zaharaddeen Sani, Adam Zango, Mustapha Naburaska, Horo Danmama da dai sauransu.