Masu garkuwa da mutane sun gudu da Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Sumaila da Takai na jihar Kano, Honorabul Garba Durbunde.
Rahotannin da ba a kai ga tabbatar da su ba sun ce an sace shi ne a ranar Talata, a kan hanyar Kaduna, bayan da ya kuma sammako ya bar Abuja. Premium Times ta ji cewa an yi garkuwa da shi ne kafin ya kai Jere, a kan hanyar sa ta zuwa Kano a ranar da abin ya auku.
Mai magana da yawun mambobin majalisa, Hon. Namdas, ya ce ba shi da labari. Sai dai kuma wani Dan Majalisa da ba ya so a bayyana sunan sa, ya tabbattar da sace wakilin na Takai da Sumaila, kuma ya ce iyalan san a tuntubar wadanda suka yi garkuwar da maigidan na su. Haka shi ma mai taimaka wa Dan Majalisar, wato hadimin sa a ofis, Tunde Adela, ya tabbatar da garkuwar da aka yi da shi.
Wata majiya kuma ta ce jami’an tsaron farin kaya, SSS sun tsunduma kan bincike.
Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje, ya yi tir da garkuwar da aka yi da Durbunde, inda ya nuna fushi da jimami, kana kuma da nuna cewa keta ce. Ya yi kira ga jami’an ‘yan sanda su hanzarta cewa Dan Majalisar wanda rahotanni suka nuna cewa tun wajen 5 na asuba ne ya bar Abuja a ranar Talata domin hanzarin zuwa Kano.
Ganduje kuma ya yi kira ga jama’a da su rika yin kaffa-kaffa yayin zirga-zirga.