Musulmai da ke Azumin watan Ramadana a jihar Kaduna sun roki gwamnan jihar Nasir El-Rufai da ya taimaka ya raba wa talakawa kayayyakin abinci ko da na buda baki ne.
Da yawa daga cikin wadanda suka tattauna da gidan jaridar PREMIUM TIMES sun roki gwamnan da ya taimaka ya duba irin halin da mutane suke ciki ya dan taimakamusu ko da da wuraren bude baki ne a jihar kamar yadda wasu gwamnonin jihohi suke yi.
Kafin zuwan wannan gwmnati, mutanen jihar sun saba da samun dan taimako na kayan masarufi musamman idan wata irin haka ya kama daga gwamnati.
Gwamnati mai ci yanzu ta dakatar da yin hakan inda ta koka da rashin kudi.
A shekarar 2015 El-Rufai ya sanar wa wata tawagar kungiyoyin Kiristocin Najeriya CAN da na Jama’atul Nasuril Islam a wata ziyara da suka kai masa cewa daga wannan shekarar gwamnati ba za ci gaba da yin irin wadannan ihsani da take yi ba.
” Na san cewa a lokacin watan azumin Ramadan gwamnati kan taimaka wa mutane da kayayyakin abinci amma mu ba za mu yi haka ba saboda bai kamata gwamnatin jihar na shiga sha’ani na addini ba sannan kuma jihar na fama da karancin kudi.”
PREMIUM TIMES ta ziyarci wasu kananan hukumomi a jihar Kaduna da ya hada da Zariya, Birnin- Gwari da Kubau inda mazauna garuruwan da muka ziyarta suka yi kira ga gwamna El-Rufai da ya sassauta akan wannan shawara nasa ya dan taimaka wa mutanen jihar da kayayyakin masarufi a wannan lokaci da ake azumi.
Wani magini mazaunin unguwanTudun-Wadan Kaduna yace ‘’mun san yace ba zai yi amfani da kudin gwamnati ba domin ya agaza wa mutane amma muna rokonsa da ya canza wannan ra’ayi nasa ya taimaka”.
Hajiya Laure mazauniyar Kofa a Zariya ta ce ” a gaskiya azumin bana ya yi wuya wa mutane da dama a Zariya. Kusan mutane sama da 50 ne sukan dan leko gidana domin samun dan abin bude baki. Ina rokon gwamnati ta bude wasu wurare da mutane za su ringa zuwa domin samun abin buda baki.’’
Wani mazauni Panbeguwa a karamar hukumar Kubau mai suna Nasir Bala ya yi kira ga gwamnati da kuma attajiran dake jihar da su taimakawa talakawa musamman a wannan wata na azumin Ramadana.
” Muna matukar bukatan taimako a wannan azumin saboda hakan nake kira ga gwamnan jihar Kaduna da ya agaje mu kamar yadda jihohin Kano, Yobe,Sokoto da sauransu ke yi.”
Bayan haka wani jami’I a fadar gwamnati ya fada wa gidan jaridar PREMIUM TIMES cewa gwamantin jihar Kaduna na nan a kan bakanta na kin amfani da kudaden gwamnati domin yi wa mutane hidima irin wannan.
Jami’in ya ce gwamna El-Rufai da wadansu aminansa na taimaka wa talakawan jihar a kowani lokaci ba sai dole lokacin azumi ba.
“Gwamnatin jihar Kaduna baza ta yi amfani da kudaden jama’a ba domin yin amfani dasu wajen yin hakan. Yace akwai wata gidauniya mallakra gwamnan wanda yake taimakawa mutane da shi maisuna El-Rufa’I foundation.’’