Hukumar kiwon lafiya ta Duniya, WHO, ta bayyana cewa illolin shan sigari na kawo karshen rayuwar mutane sama da milyan bakwai a kowace shekara, yayin da ake kashe Dala tiriliyan 1.4 a kan harkokin lafiyar da suka jibinci ciwukan da illar shan sigari kan haddasa, a kowace shekara.
Darakta Janar na WHO, Margaret Chan ce ta bayyana haka a wani sharhin bin didigin cutar da shan sigari kan haddasa, a Ranar Sigari ta Duniya, a yau Laraba.
Yin watsi da shan sigari kwata-kwata zai kawo karshen kisan milyoyin mutanen da ke mutuwa sanadiyyar cutar shan ta, kuma zai raga radadin talauci ga masu karamin karfi.
‘’Cutar sigari ba karamar illa ba ce kuma ta na kawo mana barazana, sannan kuma ta na gurbata iskar da muke shaka.
Daga nan kuma sai hukumar ta yi kakkausan kira ga gwamnatocin kasashen duniya da su saka takunkuminn saida sigari da yin tallar ta, ko yayata wani samfur daga nau’o’in ta.
Discussion about this post