Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya karyata korafin da janar Ishaya Bamaiyi ya yi a kansa cewa wai gwamnatin sa ta yi farautar ran sa a wancan lokacin.
Obasanjo ya fadi hakan ne da ya ke zantawa da kungiyar ‘yan Jarida a jihar Ogun.
Yace gwamnatin sa ta nemi Bamaiyi da ya wanke kansa ne akan zargin da akeyi masa na hannu da yake dashi a mutuwar wasu ‘yan Najeriya.
” Da ya ce wai ina neman in kashe shi, bai yi tunanin wadanda shi ya kashe ba. Ya sani cewa gwamnati na ba ta ne mi kashe shi ba.
” Abin da muka nema a wancan lokacin shine ya yi wa gwamnati bayani akan zargin da ake yi masa cewa wai ya kashe wasu ‘yan Najeriya. Wanda hakan kuma tsari ce da bai saba ma doka ba.
” Wa ye shi da zai ce wai ina son in kashe shi. Shi wa ye? Ribar mene ne zan sa mu idan nayi hakan.”
Tsohon Hafsan Hafsoshin sojojin Nijeriya, Janar Ishaya Bamaiyi, ya bayar da labari yadda manyan hafsoshin kasar nan suka rika tafka rikici, tuggu da tirka-tirkar wanda zai zama shugaban kasa bayan mutuwar tsohon shugaban kasa, Janar Sani Abacha, wanda ya mutu ranar 8 Ga Yuni, 1988.
Bamaiyi, wanda tsohon Laftanar Janar ne, ya bayyana wannan kwamacala ce a cikin wani littafi da ya rubuta da Turanci, mai suna “Vindication of a General” wanda aka kaddamar a ranar Alhamis da ta gabata, a Abuja.
A littafin Bamaiyi ya ce Obasanjo ya nemi ganin bayan sa lokacin da yake shugaban cin Najeriya.