Mazauna unguwan Kubwa sun koka da biyan kudi da suke yi kafin su sami rigakafin Sankarau

0

Wasu mazauna unguwan Kubwa dake babban birnin tarayya, Abuja sun koka da yadda sai sun biya kudade kafin su sami rigakafin cutar sankarau a cibiyoyin da gwamnati ta kakkafa a garin.

Mazaunan unguwan sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN cewa bai dace a ce wai sai sun biya kudade ba kafin su sami rigakafin maimakon abasu kyauta.

Bincike ya nuna cewa wata kungiya ce da ke zaman kanta mai suna Maladitrace Foundation ke karban kudade a hannun marasa lafiya kafin ta basu wannan rigakafin.

Wani mazaunin unguwan mai suna Tony Isibon ya ce bashi da tabbacin cewa rigakafin daga gwamnati take.

Tony yace shi ya biya kudaden (N500) ne domin haka yaga kowa na biyu.

Ma’aikaciyar kungiyar Maladitrace Foundation Magaret Gonga ta ce tabas sai an biya kudi kafin ake samun alluran rigakafin kuma suna karban kudin ne domin taimaka wa mutane su sami rigakafin cutar.

Shugaban hukumar cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na Abuja Rilwanu Mohammed yace hukumar su ba su da wata masaniya akan abin da ya ke faruwa.

Ya kuma tabbatar da cewa alluran rigakafin da gwamnatin ta bada sun kare wanda hakan ya sa suka dakatar da aikin.

Daga karshe shugaban hukumar bai tabbatar da cewa ko hukumar za ta bincike ingancin alluran da kuma dalilan da ya sa ake karban kudi.

Share.

game da Author