Duk da hani da akayi na a daina amfani da maganin zazzabi, Chloroquine, mafi yawa-yawan ‘yan Najeriya na amfani dashi har yanzu

0

Shekaru 11 kenan da kasa Najeriya ta sanar da hana amfani da maganin cutar zazzabin cizon sauro mai suna chloroquine saboda bayanan da kwararru suka bada cewa maganin na da illa sannan kuma baya warkar da cutar zazzabin cizon sauron.

A dalilin haka gidan jaridar PREMIUM TIMES ta gudanar da wata bincike akan ko mutane sun guji maganin ko kuma suna nan suna amfani dashi domin warkar da cutar.

Sakamakon binciken ya nuna cewa har yanzu fa mutane na yin amfani da maganin domin warkar da cutar zazzabin cizon Sauro idan sun kamu.

Kamar yadda bincike ya numa, a shekarar 2005 ma’aikatar kiwon lafiya ta kasa ta hana amfani da maganin bayan hukumar kiwon lafiya na dinkin duniya ta shawarce ta akan hakan.

Dalilin da ya sa kasa Najeriya ta yi hakan shine ganowa da akayi cewa maganin baya warkar da cutar zazzabin cizon sauro duk da cewa maganin na warkar da wasu cututtuka.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta gudanar da gwaji akan ingancin maganin a shekara 2002 inda ta gano cewa maganin na iya warkar da cutar zazzabin cizan sauro da ya kai kashi 35 bisa 100 ne kawai.

Hukumar kula da abinci da magunguna ta Najeriya NAFDAC ta ce tana yi wa maganin rajista domin a binciken ta ta gano cewa maganin na warkar da wasu cututtuka da ba zazzabin cizon sauro ba.

A shekarar 2014 hukumar NAFDAC ta fadi a wata rahotan ta cewa maganin ya fara bace wa a kasa Najeriya duk da cewa bayan bincike da muka gudanar akan hakan kusan ko wani shago da muka bincika yana siyar da wannan magani na chloroquine.

Da muka yi hira da wani ma’aikacin kamfanin sarrafa magani na ‘Dana Pharmaceuticals’ ya ce har yanzu kamfanin Dana din na sarrafa maganin chloroquine amma ba don warkar da cutar zazzabin cizon sauro ba sai dai don wasu cututtukan da suka gano yana warkar wa.

Ya ce duk da haka ba za a rasa mutanen da ke amfani da maganin ba domin warkar da cutar zazzabin cizon sauro ba.

Wata mata da take da shagon siyar da magunguna Celine Egbuchulem ta ce tana amfani da maganin ma kanta domin warkar da cutar zazzabin cizon sauro kuma tana siyar wa mutanen da ke bukata.

Bayan taron kiwon lafiya na duniya na karo 30 da aka yi a shekarar 2007 Najeriya da sauran kasashen duniya sun amince da hana siyar da maganin chloroquine din.

Gidan jaridar PREMIUM TIMES ta tambayi darektan aiyuka da sadarwa na hukumar NAFDAC Abubakar Jimoh ko suna yi wa maganin rajista a hukumar tasu har yanzu.

Jimoh yace hukumar NAFDAC din na yi wa maganin rijista har yanzu.

Ya ce dalilin da ya sa suke yi wa maganin rajista shine domin maganin na warkar da wasu cututtuka kamar cutar ciwon kafa wanda ake kira da turanci ‘Rheumatoid Arthritis’ sannan kuma da wasu cututtukar dake kama hanjin mutum.

Daga karshe Jimoh yace hukumar ta na ta kokarin wayar wa mutane kai akan illar amfanin da maganin wajen warkar da cutar zazzabin cizon sauro.

Share.

game da Author