Hukumar Kula da masu bautar kasa, NYSC ta sanar da cewa ta na aiki sosai domin ganin an sake bude sansanin masu bautar kasa a Maiduguri, ganin cewa a yanzu an samu dawowar zaman lafiya a jihar.
Darekta Janar na NYSC, Sulaiman Kazaure ne ya fadi haka ranar Talata yayin da ya ke zantawa da ’yan jarida a Maiduguri.
Kazaure ya kara da cewa hukumar ta kagara matuka wajen ganin ta sake bude sansanin ta na Maiduguri, tunda za a iya cewa an samu zaman lafiya a jihar.
“Yanzu an samu zaman lafiya a jihar, don haka za mu so mu sake dawowa mu bude sansanin mu. Sai dai kuma kada ku manta, har yanzu ‘yan gudun hijira na nan damfare a sansanin masu bauta wa kasa din.” Inji Kazaure.
Ya kara da cewa za a bude sansanin da zarar an kwashe ‘yan hijirar da ke zaune a cikin sansanin.
“A jihar Barno ne kadai NYSC ba su cikin na su sansanin. Amma a shirye muke a duk lokacin da gwamnatin jihar Barno ta damka mana sansanin na mu, to za mu yi gaggawar kawo masu bautar kasa da suka kammala jami’o’i a ciki.”
A karshe Kazaure ya jinjina wa masu bautar kasa da ke gudanar da ayyukan su a jihar, saboda kwazon su da kuma nuna juriya.