Cibiyar Binciken Labarai Da Bayanai ta Premium Times, wato PTCIJ, ta kaddamar da na’urar tantancewa da kula da kiwon lafiya a matakin farko, wato Primary Health Care, a matsayin wani hangen nesa wajen yin amfani da fasahar zamani domin magance matsalar rashin ingancin kula da lafiya a Nijeriya.
Ita dai wannan na’ura mai suna PTC Tracker, ana sarrafa ta ne a yanar gizo sannan an samar da ita ne domin zama hanya mafi saukin tabbatar da cewa ayyukan kula da lafiya a matakin farko na kaiwa ga jama’a, ta hanyar kididdige komai a kan ka’ida, yadda al’umma za su iya sanin yadda gwamnati ke gudanar da aiki a fannin kiwon lafiya.
Haka kuma wannan na’ura za ta samar wa jama’a da ‘yan jaridu hanyar samun rahoton fannin lafiya da sauran ayyukan da gwamnati ke gudanarwa wadanda suka jibinci kula da lafiya.
Shugaban Cibiyar Dapo Olorunyomi, ya ce ‘Wannan wata hanya ce da bin diddigin yadda gwamnati ke aiwatar da manyan ayyukan kula da lafiya ta yadda jama’a za su san komai da komai. Ba ma kawai sa-ido ba, har ma domin tabbatar da karin kaimin gwamnati wajen kara kulawa da kiwon lafitya.’
Ya kara da cewa, ‘Yin amfani da wannan sabuwar hanya zai tabbatar da kawo sabon sauyin ci gaba a fannin kula da lafiya, kuma zai kara wa jama’a kwarin guiwar sanin abin da ake samar musu a yankunan su.”
Wannan na’ura dai wata sabuwar kirkirarrar fasaha ce da aka samar ta hanyar hadin-guiwa tsakanin PTCIJ da Dode for Nigeria tare da goyon bayan gidauniyar agaji ta Bill and Melinda Gates Foundation, BMGF.
Sabuwar fasahar dai an samar da ita ne sakamakon kyakkyawar kudiri, muradi da tsarin PTCIJ na samar da hanyar da za ta taimaka wajen magance matsalolin da suka yi wa kasar nan katutu a fannin al’amurran tafiyar da rayuwa.
Da ya ke jawabi, darektan kula da cibiyar ta PTCIJ, Joshua Olufemi, ya nemi ‘ jama’a da su tashi haikan wajen maida hankali kan wannan tsari ta yadda za su rika bayyana ra’ayin su dangane da halin da su ke ciki dangane da lafiyar su da kuma sauran cibiyoyi ko asibitocin kula da lafiyar su.a fadin kasar nan.”
Ya kuma shawarci jami’an kula da lafiya da ‘su yi amfani da wannan hanya wajen kai rahotanni ba tare da tsoro ko shakkun kuntata musu ba, saboda rahotan na su zai kasance na sirri ne, sai fa inda wani mutum ya amince a bayyana kawai.”
ita dai wannan na’ura, an samar mata dabarun tsarin gano daidai wuraren da wasu wurare ko kayyaykin kula da lafiya suke, wanda hakan zai samar da hanyoyi masu sauki wajen tantancewa ko kai ziyarar shi mai tantancewar ko kai rahoton.
Olufemi ya kara yin kira ga masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya da su nemi yin hadin guiwa da PTCIJ, a matsayin wata hanyar kaiwa gacin tabbatar da wanzuwar alfanun da ke tattare da fannin kiwon lafiya.
Za a iya samun damar sanin wannan na’ura ta: www.phc.ptcij.org, kuma za ta iya amfani a kowace irin wayar selula ta zamani.
Discussion about this post