Yau Talata da misalin karfe 9:10 na safe ne gobara ta tashi a ofishin kula da jarabawar sakandare ta WAEC na shiyyar Kaduna.
Wani babban mai tsaron ofishin ya shaida wa wakilinmu cewa wutar ta tashi ne daidai karfe 9:10 na safe, a ofishin da ke kan titin Zaria Road, a Kawo, Kaduna.
“Mun samu kiran gaggawa da safiyar nan cewa gobara ta tashi a inda ta ci wasu ofisoshi na hukumar kula da jarabawar kammala sakandare, wato WAEC, da ke nan Kaduna.”
“Wutar ta lalata ofisoshi hudu, amma jami’an kashe gobara da sauran jami’an tsaro sun yi saurin shawo kan wutar.”
Ya kara da cewa suna zargin wutar ta faru ne sanadiyyar matsalar wayoyin wutar lantarki.
Kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna, Aliyu Usman ya ci tura, domin ya ki daukar kiran wayar sa da aka yi.
Haka kuma sakon wasika da aka tura masa ta wayar sa ita ma, duk bai maido amsa ba.
Sai dai kuma wani jami’in hukumar WAEC da ba ya so a fadi sunan sa, ya shaida wa ‘yan jarida cewa wutar ta shafi ofishin tattara bayanan sakamako da shirya jarabawa na hukumar.