Jaruma ‘yar wasan fina-finan Hausa Nafeesat Abdullahi ta sanar da dawowarta harkar fina-finan Hausa bayan bacewa bat da tayi a farfajiyar.
Nafeesat ta sanar da hakan ne a shafinta na Instagram in da ta saka wata hotonta na wani fim da ta fito a ciki.
Nafeesat ta rubuta cewa “ Na gama hutun, na dawo, duk da cewa dama can ban tafi ko ina ba.