Kungiyar likitocin hakora na kasa ta shawarci ‘yan Najeriya da su yawaita tsaftace hakoran su

0

Kungiyar likitocin hakora na kasa NDA ta ce ya kamata yawaita wayar da kan mutane akan mahimmancin taftace hakora, illolin da ke tattare da rashin taftace hakora da kuma asibitocin da za a iya zuwa idan an samu matsala a hakora.

Kungiyar ta fadi hakan ne a taron ranar kula da hakora wanda ake yi a kowani watan Maris din duk shekara a Abuja.

Kamar yadda bincike ya nuna mutane sama da biliyan 3.9 a duniya ne ke fama da matsalolin da ke tattare da rashin tasftace hakora ba tare da sun sani ba.

Mataimakiyar shugaban kungiyar Funmi Ashiwaju da take bada nata jawabin a taron da ke da taken ‘’Live Mouth Smart’’ ta ba da shawara da mutane su ringa tsaftace hakoransu a koda yaushe domin samun lafiyar hakoran.

Ta kuma kara da cewa saboda hakan ne kungiyar ta amince da ta hada karfi da karfe da wasu kungiyoyi na duniya domin wayar da kan mutane da yara a makarantu akan mahimmancin tsaftace hakora da kuma inda za a sami ingantacciyar kula.

Bayan haka gidan jaridar PREMIUM TIMES ta yi hira da wasu mazaunan babban birnin tarayya Abuja akan tsaftace hakora. Wata Iyabo ta ce ta dade tana fama da rami a hakorin ta kuma ta kasa zuwa asibiti domin tsadan da wasu asibitocin da suke zaman kansu suke da shi sannan a asibitocin gwamnatin da ake samu da arha mutane sun yi musu yawa.

Wani likitan hakora a Abuja Kenneth Ighalo yace mutanen Najeriya basu damu da su tsaftace hakoran suba sai lokacin da suka sami matsala sannan suke neman magani.

Ya kuma kara da cewa rashin sani ne yake kara ingiza mutane yin amfani da magungunan gargajiya domin a ra’ayinsa babu yanda za a yi tsutsa ya fito daga cikin hakori da irin wadannan hikima da suke amfani dasu.

Mataimakiyar shugaban kungiyar Ashiwaju ta ce dalilin da ya sa wasu asibitocin ke da tsada shine saboda na’urorin da suke amfani da su na da tsadan gaske.

Duk da hakan ta ce a asibitocin gwamnati akwai kwararrun likitoci wanda mutane zasu iya samun kula akan cwon hakora.

Daga karshe shugabannin kungiyar sun shawarci jama’a da su gaggawta zuwa asibitocin kula da hakora da cututtukan da ya shafi hakora domin gujewa samun matsala a hakoransu.

Share.

game da Author